Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin jihar Kano da gaggauta tallafawa mutane da iftila’in gobarar Kwalema ta shafa don inganta rayuwarsu.
“Ina kira ga gwamnan jihar Kano da ya gaggauta fara gudanar da cikakken bincike kan musabbabin faruwar wannan gobara domin hana afkuwar irin wannan a gaba. Bugu da ƙari, ina kira ga gwamnati da ta ba da agajin gaggawa da tallafi ga wadanda abin ya shafa tare da aiwatar da matakan dakile sake faruwa a nan gaba”.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Alhaji Atiku Abubakar ya wallafa a sashin shafinsa na Facebook da safiyar ranar alhamis din nan.
“Na yi matukar bakin ciki da yadda wata gobara ta tashi a wata karamar masana’anta da ake sarrafa kayayyaki da kasuwanci da ke unguwar Dakata a Jihar Kano da safiyar ranar Larabar da ta gabata”.
Iftila’i: Gobara ta Kone Kasuwar Yan Gwan-Gwan da ke Kano
Ina addu’ar duk wadanda suka rasa dukiyoyinsu da rayuwarsu a wannan lamari mai cike da takaici Allah ya mayar musu, Tabbas an yi asarar biliyoyin nairori, wannan babban rashi ne, ba wai ga wadanda abin ya shafa ba, har ma ga daukacin al’umma.