A wani yunkuri na taimako da jin-kai ga marayu da masu karamin karfi kungiyar Salanta A Yau, ta rabawa yara maza da mata sama da 200 tallafin kayan Sallah domin gudanar da bukukuwan sallarsu kamar yadda kowa da kowa yake gabatarwa.
An gudanar da rabon kayan sallah ne a tsakiyar cikin unguwar Salanta kan Labi a safiyar wannan rana ta Talata, tun da fari da yake jawabi a wajan taron shugaban kungiyar ta Salanta a Yau Malam Ahmad Muhammad Mika’il ya bayyana cewa,makasudin shirya taron wannan na daya daga cikin manufofin kungiyar musamman bangaren taimakawa yara marayu da marasa karfi.

Shima da yake nasa jawabin mai unguwar Dukawuya Salanta Malam Magaji Garba ya nuna jin dadinsa da wannan tallafin da kungiyar ta bayar tare da yin kira ga dukkanin alummar unguwar musamman masu hannu da shuni dasu cigaba da tallafawa yunkurin wannan kungiya da dukkanin abun data ke bukata domin gudanar da harkokinta na yau da kullin.
Bincike: Shin Sabon Hakimi ya shiga gidan sarautar Bichi kuwa ?
Daga karshe iyayen marayun da suka rabauta da wannan kayan wacce Hadiza Isyaku Abdullahi ta tayi jawabi a madadin iyayen marayun ta nuna farin cikinta ga iyayen kungiyar ta Salanta A Yau.
Taron da ya samu halaltar masu rike da sarautun gargajiya malamai da sauran mutum unguwannin Salanta Gidan Tudu Salanta Sabon Feggi da dai sauransu.