Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin baiwa sarakunan Kano da hakimai dukkanin goyon bayanl da gudunmawar da su ke bukata domin gudanar da hawan sallah karama.
” Shi mutumin kano babu abun da yake so bayan kammala azumin watan Ramadana,illa sallah ta zo ya caba ado ya fito domin ya gaishe da Sarkinsa , shi kuma Sarkin ya yi masa addu’a”.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na wannan jawabi ne yayin da yake gabatar da shan ruwa da sarakunan a fadar gwamnatin a yau talata .

Gwamnan ya ce yana kira ga sarakunan Kano Rano Gaya da Karaye da su da hakimansu da su fito domin gudanar da bukukuwa hawan sallah kamar yadda aka saba.
Yanzu-yanzu: Tinubu ya aiyana dokar ta baci a jihar Rivers
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a shekarar da ta gabata da Babbar sallah ba a gudanar da hawan sallah a Kano ba , saboda rikicin Masarautar Kano da yanzu haka yake gaban Kotu.