Kungiyar APC Patriot Volunteer ta taya shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje murnar sake ba su damar cigaba da shugabantar jam’iyyar har zuwa shekara ta 2026.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa Alhaji Usman Alhaji ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito masu ruwa da tsakin jam’iyyar karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu sun nuna amincewar da Ganduje ya cigaba da jagorantar jam’iyyar.
Sanarwar ta ce Wannan gagarumar nasara ce da zata taimaka wajen cigaban jam’iyyar APC a Nigeria.
” Tabbas Ganduje ya chanchanci ya ci gaba da Shugabantar jam’iyyar APC saboda yadda ya hade kan yan jam’iyyar da kuma yadda jam’iyyar ta sami nasarori a zabukan cike gurbin da aka yi a Jihohin Imo Kogi da Ondo .
Shekarau ya magantu kan batun sake hadewarsu da Kwankwaso
Haka zalika, sanarwar ta kara da cewa daga cikin nasarorin da Ganduje ya samu har da karbo jiga-jigan wasu yan jam’iyyun adawa zuwa APC.
Sanarwar ta kuma taya al’ummar Musulmi murnar shigowar azumin watan Ramadana, sannan ta yi fatan Allah ya karbi ibadu ya kuma karawa jam’iyyar APC nasara.