Muhimmin Sakon Murtala Sule Garo ga Al’ummar Jihar Kano

Date:

 

Assalamu alaikum wa Rahmatullah

Ina mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya daban-daban su ka fara gudanar da azumin watan Ramadan.

Tabbas wannan babbar dama ce a garemu ta inganta alakarmu da Allah maΙ—aukakin sarki ta hanyar habaka ibadarmu da neman yafiyarsa.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ina amfani da wannan dama wajen kira ga al’ummar musulmi dan yin koyi da dabi’un annabin rahama amincin Allah ya tabbata a gareshi wajen nuna tausayi da jinkai da karamci da kuma taimakawa marasa karfi.

Wannan wata mai alfarma dama ce ta tunawa da marasa karfi a cikinmu tun daga ‘yan uwa da makwafta har izuwa sauran al’umma.

Shekarau ya magantu kan batun sake hadewarsu da Kwankwaso

Hakazalika ina kira ga al’ummar jihar Kano da su dukufa wajen addu’o’in zaman lafiya da cigaba da yalwar arziki.

Ina yi wa kowa fatan alkairi. Allah ya karbi ibadinmu ya kuma sa mu kasance cikin bayin da zai yanta. Amin

Ramadan Kareem, Jumu’at Mubarak!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related