Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi ganawarsa ta farko a da kungiyar wakilan kafafen yada labarai reshen jihar Kano.
Da yake jawabi yayin taron, Kwamishinan ya bayyana cewa, manufarsa ita ce tattaunawa da kungiyar don karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninsu.

Waiya ya bayyana wakilan kungiyar a matsayin ’yan jarida masu bin ka’ida da kwarewa wajen gudanar da ayyukansu.
Kwamishinan ya amince da gudunmawar da kungiyar masu aiko da rahotanni ke bayarwa wajen sanar da jama’a ayyukan gwamnati da shirye-shiryenta.
Jimami: Hadimin Gwamnan Kano ya Rasu
A nasa jawabin shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labaran reshen ta jihar Kano, Aminu Garko, ya bayyana jin dadinsa bisa yadda kwamishinan ya nuna gamsuwa da irin aiyukan da suke yi wajen fadakar da al’umma kokarin gwamnatin jihar Kano.
Ya kuma tabbatar wa da Kwamishinan a shirye su ke su hada kai da ma’aikatar wajen yada sahihan bayanai masu inganci ga jama’a bisa ka’idojin aikin jarida.