Daga Tijjani Sarki
Wasu daga cikin Kungiyoyi masu zaman kasansu sun yaba da matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na tantance aiyukansu a jihar.
Mataimakin shugaban kungiyar Human Rights Watch and Youth Empowerment Foundation, Nigeria Tijjani Sarki ne ya bayyana hakan Jim kadan bayan da gwamnatin ta kaddamar da kwamitin.
Ya ce tabbas Wannan matakin zai taimka sosai wajen magance wasu matsaloli da ake zargin Kungiyoyi masu zaman kasansu na haifarwa.

“Idan aka yi la’akari da zargin daukar nauyin taa’addanci da ake yiwa kungiyar raya kasashe ta Amuruka wato USAID , a iya cewa gwamnatin Kano ta yi abun da ya dace a sanda ya dace”.
Ya ce tantancewa da bibiyar aiyukan Kungiyoyin zai taimakawa gwamnatin ta fitar da duk wata kungiya da ta ke gudanar da aiyukan da za su cutar da al’umma ko da a gaba.
Gwamna Abba ya Rantsar da Sabon Sakataren Gwamnatin Kano
Tabbas Gwamnatin jihar Kano ta yi farar dabara, domin in har wannan kwamiti zai gudanar da aikin da aka dora masa to za a fitar da bara gurbi daga cikin Kungiyoyin farar hula a Kano.
A tunanina bai kamata Kungiyoyi masu zaman kasansu a Kano su damu da wannan matakin ba saboda zai taimakawa wajen inganta aiyukan Kungiyoyin na gaske da kuma fidda bara gurbin cikinmu.
Tijjani Sarki
Mataimakin shugaban kungiyar Human Rights Watch and Youth Empowerment Foundation, Nigeria