Daga Sharifiya Abubakar
Kungiyar ‘yan majalisun dake kula da tsaro da bayanan sirri ta duniya (PI-SF) ta nada tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, matsayin Daraktan Hulɗa da ‘yan majalisar Afrika kuma memba a kwamitin zartarwa na kungiyar.
Nadin nasa na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na duniya dan majalisar Amurka Robert Pittenger ya sanyawa hannu ranar 4 ga Fabarairun 2025.

Sanarwar ta kara da cewa, jajircewa da kuma kwarewarsa wajen bunkasar harkokin tsaro a fadin duniya ya sanya ya zama mafi chanchanta da mukamin.
Dan Majalisar NNPP ya fice daga jam’iyyar zuwa APC
Darakta Sha’aban zai mayarda hankali wajen Inganta hulɗa da haɗin gwiwa tsakanin shugabannin majalisun Afrika don tunkarar matsalolin tsaro da gudanarwa, hadi da kawo ƙarin ‘yan majalisa, jami’an tsaro, da masu tsara manufofi daga Afrika cikin tarukan kungiyar.
Kazalika sabon daraktan zai samar da fagen tattaunawa tare da majalisun Afrika don inganta haɗin kai kan tsaro, leƙen asiri, tsaron yanar gizo, da sauransu.