Ma su shirya wa shugaban NAHCON, Farfesa Abdullah maƙarƙashiya da makircinku ba zai yi nasara ba – In ji Musa Iliyasu Kwankwaso

Date:

 

 

Babban Daraktan kudi na hukumar raya kogunan Hadeja-Jama’are kuma jigo a jam’iyyar APC Musa Iliyasu Kwankwaso, ya yi gargadin cewa makircin karkatar da hankalin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a shugaban hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) daga aikinsa ba zai yi nasara ba.

Kadaura24 ta rawaito Kwankwaso ya mayar da martani ne a kan wani labari da ke cewa maniyyatan Najeriya ba za su yi aikin Hajjin 2025 saboda wasu dalilai ko gazawar shugaban hukumar.

Ya ce wannan batu an kirkireshi ne kawai don a kawo ruɗani a ayyukan da sabon shugaban ya sa a gaba don ganin an samu nasarar aikin a bana.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sannan kuma ya ce ana haka ne don a kawo cikas ga gwamnatin Tinubu.

” Mun fa san komai, wasu makiya ne suka sa hukumar da shugabanta Farfesa Abdullahi a gaba saboda ya na kawo sauye-sauyen masu alfanu da ba su za ta a iya kaiwa ga su ba cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ba. Suna so su dama masa lissafi da gangar don su dagula tafiyar da ake samun nasarori akai karara kowa na gani.

Inganta Ilimi: Abba Bichi ya dauki sabbin malamai 200 aiki

Haka kuma muna sane cewa an yo hayan wasu marubuta su rika sukar ayyukan hukumar ƙarƙashin shugabanta Farfesa Abdullahi. Toh su sani hakarsu ba zai cimma ruwa ba.

” Ina so in sanarwa maniyyar da su toshe kunnuwarsu, ina mai tabbatar musu da cewa za ayi hajjin da ba a taɓa yin irinsa ba saboda kyawunsa na nagartarsa ƙarƙashin shugabanta Farfesa Abdullahi Pakistan.

Masu kokarin kawo masa matsala kuma za su gani a kwaryarsu.

A cikin wannan mako an samu wasu da suka zargi shugaban NAHCON, da yin gaban kansa wajen saka hannu a wasu kwangilolin masu hidima ga mahajjata a Masha’ir. Wannan zargi ya fito ne daga wai wasu daga cikin shugabannin hukumomin Alhazai na jihohi.

Sai dai tun bayan haka, Farfesa Abdullahi ya ƙaryata wannan batu in da ya bayyana cewa ba zai yi abinda ba zai kawo wa hukumar batanci a idon mutane da maniyyata ba.

Sannan kuma ya karyata masu jita-jitan wai ƴan Najeriya za su rasa Biza a bana.

Haka shi ma mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jaddada cewa babu wani maniyyaci daga Najeriya da zai rasa zuwa hajji a bana. Komai na tafiya yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...

Rasuwar Aminu Dantata: Duniyar Kasuwanci ta yi Babban Rashi – Shugaban Kamfanonin Gerawa

Shugaban rukunonin Gerawa group of Companies Dr. Ibrahim Muhammad...

Da dumi-dumi: Wasu kungiyoyin APC a Kano sun fara kiraye-kirayen Abdullahi Abbas ya sauka daga shugaban jam’iyyar

Daga Hafsat Abdullahi Muhammad Kungiyoyin jam'iyyar APC da suka hadar...