Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, Ambasada Ahmadu Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya.
Daya daga cikin maβaikatan hukumar ne ya shaidawa manema labarai rasuwar Dan Zago din.

Ya ce za a yi jana’izar sa a gidan sa da ke Kurna, Tudun Bojuwa, kusa da Kunya Chemist a yau Alhamis da misalin Ζarfe 1 na rana.
Dan Zago dai fitaccen dan siyasa ne a jihar Kano, wanda da shi aka riΖa yakin neman zaben tsohon shugaban Ζasa Muhammadu Buhari.
A ranar 5 ga watan Yulin 2023 ne gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nada Haruna Zago a matsayin Shugaban hukumar kwashe shara ta Kano.