Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Shugaba Bola Tinubu ya umurci dukkan ministocin gwamnatinsa da su gaggauta fitowa domin su bayyanawa al’ummar Nigeria aiyukan da suka a ma’aikatun da aka turasu.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris ne ya sanar da umarnin shugaban kasar a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
Yanzu-yanzu: Sarkin Rano ya dakatar da harkokin ibada a wata Coci dake cikin garin Rano
Ministan ya ce bayanin da ministocin za su yi shi ne zai baiwa ‘yan Najeriya damar sanin abubuwan da gwamnati ta yi da kuma yin tambayoyi a akan abubuwan da ba su fahimta ba.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito dama shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ce wajibi ne duk bayan watannin shida ministocin su rika fitowa suna bayyanawa al’ummar Nigeria aiyukan da suke gudanarwa a ma’aikatunsu.