Muna bukatar gwamnatin Kano ta tallafa mana da ababen hawa don inganta tsaro a Kano – Kwamandan Vigillante

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

Kungiyar yan Vigillante ta yi kira ga gwamnati jahar kano da ta tallafawa jami’an kungiyar da kayan aiki don inganta aiyukansu a lungu da sako na jihar baki daya.

Kwamandan shiyyar na karamar hukumar Nasarawa Samaila Abdu Dakatab ne ya bayyana hakan a wata ganawa da wakilinsa Kadaura24.

Da yake bayyana irin nasarori da suka samu da kuma kalubale a wannan sabuwar shekarar da ta shigo, ya ce nasarorin da suka samu shi ne dakile fadan daba da kwacen Waya da Kuma haurawa mutane gidaje da dai sauran su a karamar hukumar Nasarawa da ma jahar kano Baki daya.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya ce wannan nasarar ta samu ne da taimakon al’ummar unguwani da kuma kokarin kwamandansu na jihar kano Alhaji shehu Rabi’u da kwamishinan yan Sanda na jahar kano da sauran DPP-DPO da suke a karamar hukumar Nasarawa da ma jahar kano.

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Ya kara da cewa kalubalen da suka fuskanta Bai wuce matsalar abun hawan da za su shiga lungu da sako domin Kamo ma bata gari ba, yace wannan babban Kalu balene da suke fuskanta a duk lokacin da za su fita aiki.

Daga karshe ya yi kira ga sauran jami’an vigilante da su cigaba da zage damtse wajan gudanar da aikin su ako da yaushe

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...