Gwamnatin Kano za ta tallafawa matasa 3000 da wata kungiya ke koyawa sana’o’i a Kano – Sani Danja

Date:

Mashawarcin gwamnan Kano na musamman kan harkokin matasa da wasanni Sani Musa Danja ya sha alwashin hada kai da Kungiyoyi masu zaman kasansu don inganta rayuwar matasan jihar.

” Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya damu matuka da rayuwar matasa , shi yasa gwamnatinsa ta fi mai da hankali wajen tallafawa mata da matasa don inganta rayuwarsu, da ta al’umma baki daya”.

Kadaura24 ta rawaito Alhaji Sani Danja ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar ganin yadda ake koyawa matasa 3000 sana’o’i daban-daban wanda wata kungiya mai suna 9ja food fiesta ya dauki nauyi a Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Sani Danja ya baiwa matasan tabbacin gwamnatin jihar Kano zata tallafawa matasa da kayan aikin sana’o’in da suka koya ko jari, don tabbatar da cewa al’ummar Kano sun amfana da ilimin da suka koya.

Ya ce kofar ofishinsa a bude take don hada kai da duk wata kungiya mai son ganin ta tallafawa rayuwar matasan jihar Kano kamar yadda kungiyar 9ja food fiesta ta yi.

Babban Dalilin da ya sa na Shiga Siyasa – Sani Danja

” Tun kafin na zama mai baiwa gwamnan Kano shawara akan harkokin matasa na damu matuka da al’amuran matasa da masu karin karfi domin talakawa da ya’yansu ne suke kallo fina-finai na har na kai matakin da na Kai, yanzu kuma da aikin da gwamna ya doramin , don haka dole na tsaya tsayin daka don ganin an inganta rayuwarku”.

Gwamnan Kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar 9ja food fiesta Muhammad Mustapha ya ce sun zo jihar Kano ne da nufin koyawa matasa maza da mata 2000 sana’o’i , amma daga bisani suka ga akwai bukatar kara adadin zuwa 3000 .

” Babu shakka wannan Aikin ne don tallafawa rayuwar matasan jihar Kano, kamar yadda muka yi a Abuja, amma mun ji dadin yadda mai baiwa gwamnan Kano shawara kan harkokin matasa da wasanni Sani Musa Danja ya ba mu duk wata gudunmawa da muke bukata don ganin an sami nasarar da muka sanya a gaba”.

Muhammad Mustafa ya yi kira ga kamfanoni da masu hannu da shuni a jihar Kano da su shigo cikin shirin don tallafawa matasan da suka gama koyon sana’o’in da jari ko kayan aikin da suka koya, don su dogara da kawunansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...