Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Date:

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan hukumomin kano da su tabbatar da sun yi aiki mai inganci kamar yadda su ka yi alkawari na tsawon shekaru 20 tare da gujewa bayar da na goro wajen bibiyar takardun kwangila.

Kwamishinan kananan hukumomin kano Hon Muhammad Tajo Usman ne ya bayyana hakan yayin da ‘yan kwangilar suka kai ziyarar aiki ofishin sa dake ma’aikatar kananan hukumomin kano.

Yana mai cewar, kafin a bayar da wani aiki a gwamnatance, an ajiye kudin da za’a biya ‘dan Kwangila hakkin sa.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya kara da cewa, ba’a yarda wani dan Kwangila ya dinga zuwa ma’aikatar kananan hukumomi domin bibiyar Fayal dinsa ba domin gudun rashawa a tsakanin ma’aikata da Dan Kwangila.

“Haka kuma akwai sabuwar ma’aikata ta musamman da gwamnatin kano ta Samar da zata dinga bibiyar aikin da aka bayar daga kananan hukumomin kano domin tabbatar da nagartar ayyukan da aka basu – “.inji kwamishinan”

Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan fitowar su, Shugaban kungiyar ‘yan kwangilar ayyukan kananan hukumomin kano 44 (Association of 44 local government contractors of Nigeria Kano State Branch) Alhaji Rabiu Aliyu Kiru ya jaddada aniyar su na kora da kuma gurfanar da duk wani Dan Kwangila daga cikin mambobin su da yayi aiki mara Inganci tare da sabunta aikin da aka bashi ba tare da an sake biyan kudin aikin ba.

Ya kara da cewa, tuni dai shirye shirye su ka yi nisa wajen fara ayyukan kananan hukumomin kano 44 domin sabunta jihar kano da manya manyan ayyukan gwamnatin kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...