Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin, ya kammala shirye-shiryen bayar da tallafin karatu ga dalibai 1,000 don yin karatun digiri a fannonin da suka shafi fasahar zamani, ICT, ƙarƙashin Gidauniyar Barau I Jibrin, BIJF.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimakawa Sanatan kan harkokin yada labarai Ismael Muddashi .
Sanarwar ta ce wadanda za su ci gajiyar shirin su ne daliban da su ka fara karatu a cibiyoyin karatu guda bakwai a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma da ke Jihar Katsina da za a kafa a mazabar Kano ta tsakiya da ta Kudu daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Ya ce Sanata Barau da mahukuntan jami’ar sun kammala shirye-shiryen kafa cibiyoyin karatu a mazabun biyu.
Matasan da Barau Jibrin ya dauki nauyin karantunsu sun bar Kano zuwa India
Sanata Barau Jibrin ya dauki wannan matakin ne a kokarinsa na tallafawa matasa Maza da mata don inganta rayuwarsu.