Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da dokar cin tarar kuɗi naira dubu 25 ga duk wanda aka samu da laifin tofar da yawu ko majina akan titunan birnin Kano.
Hakan ya biyo bayan dokar da majalisar ta amince da ita na tabbatar da tsaftar Muhalli ta cikin shirin ayyukan gyara birnin Kano da kawata shi domin samar da birni mai cike da tsafta a Najeriya.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano kuma dan majalisar Dala Hon. Lawan Husaini wanda ya yi wa manema labarai karin bayani, inda ya ce wajibi ne gwamnatin kano ta dauki matakan da suka dace wajen tsaftace birnin Kano, domin dawo da martabar birnin a idanun duniya.
Dan majalisar yace abin kunya ne da takaici yadda wasu ke yawan tofar da yawu ko face majina akan hanya duk lokacin da suka ga dama.
Sanata Barau zai baiwa dalibai 1,000 tallafin karatu a Kano ta tsakiya da ta Kudu
Ya kara dacewa majalisar daga Yanzu za’a fara cin tarar kuɗi naira dubu 25 ga wanda aka samu da laifin bayan kaishi kotu.
Radio Freedom ta rawaito cewa daga nan majalisar tayi Karatu na biyu akan yiwa hukumar kwashe shara da tsaftar Muhalli garambawul.
Daga cikin gyaran dokar hukumar ta kwashe shara harda,bukatar samar da cikakken Mataimakin hukumar da kuma bata cikakkiyar dama ta aikinta yadda ya kamata.