Tinubu ya ba da umarnin a baiwa Kwankwaso, Bichi da sauran wadanda ya nada takardun kama aiki

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta sakin takardar nadin mukamin da aka yiwa Musa Iliyasu Kwankwaso, Rabi’u Sulaiman Bichi da sauran mutane 10 da aka nada su domin jagorantar hukumomin raya kogunan kasar nan 12 .

Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a ranar 18 ga watan disambar shekarar da ta wuce shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya amince da nada su domin jagorantar hukumomin raya kogunan kasar nan dake karkashin ma’aikatar ruwa ta Kasa.

InShot 20250115 195118875
Talla

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin ne bayan wani rahoto na musamman da jaridar Tribune ta yi, kan rashin baiwa wadanda aka nadin takardar nadin mukamin da aka yi musu sama da wata daya da ya gabata.

Jaafar Jaafar ya fallasa sunan mai kitsawa gwamnatin Kano makarkashiya a Abuja

Rahotanni sun nuna cewa an rike takardaun ne bisa wasu dalilai da har yanzu ba a bayyana nasu ba, amma dai ana zargin suna da nasaba da Siyasa.

 

Rahotanni sun nuna cewa wadanda aka ki baiwa takardun kama Aikin sun yi niyyar fara aiki a makon da ya gabata duk kuwa da cewa ba a basu takardar shaidar kana aikin ba.

Kwankwaso ya yi zazzafan martani ga rundunar yansada kan Maulidin Inyass na Kano

Sun dai dauki Wannan matakin ne sakamakon wani umarni da aka basu na su je sun kama aiki daga ma’aikatar ruwa ta Kasa, inda aka ce musu za a cigaba da bibiyar lamarin idan suka kama aiki.

A wata wasika mai dauke da kwanan watan 14 ga watan janairu, 2025 da ta fito daga ma’aikatar ruwa kuma aka aikawa sabbin Shugabannin hukumomin raya kogunan, an umarce su da su je su fara aiki in yaso daga baya sai su karbi takardunsu na kama aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...