Kaso 9.6% na daliban firamare a Kano suka iya karatu – UNICEF

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce akalla Kashi 9.6 cikin 100 na daliban firamare a Kano suka iya karatu, yayin da kuma kaso 11.2 cikin 100 ne kadai suka iya mafi kankantar lissafi.

Babban jami’in aiyuka na UNICEF na Kano, Rahama Muhammad ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da suka yi a Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya ce wani bincike da suka gudanar a shekarar 2021 ya nuna cewa jihar Kano na fuskantar kalubale mai girma ta fuskantar ilimi saboda kusan yara miliyan 10 ne basa zuwa Makarantar .

Ya ce binciken ya nuna cewa akalla a cikin yara 989,234, wadanda ya kamata a ce suna zuwa Makarantun firamare, kaso 32 cikin 100 ba su sami damar zuwa Makarantu a jihar.

Babban Burina shi ne Bunkasa Rayuwar Matasan Kano – Sani Danja

Babban jami’in UNICEF ya ce UNICEF na aiki tukuru domin tallafawa harkokin karatu musamman don ganin yaran dake karatun allo kadai sun shiga Makarantu boko a jihar .

” A kokarin UNICEF na tallafawa wadancan yara, mun sauya musu manhajar karatunsu, sannan mun baiwa Malaman Makarantun allo akalla guda 290 horo na musamman a Jihohin Kano da Jigawa.

Duk muna wadannan aiyukan ne domin tabbatar da cewa yara suna zuwa Makarantu domin samun ingantaccen ilimin addini da na boko”. Inji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...