Inganta tsaro: Za mu cigaba da tallafawa yan Sanda da kayan aiki a Kano – Gwamna Yusuf

Date:

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tallafawa hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma fadin jihar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya aikowa, Gwamna Yusuf ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya karbi bakuncin uwargidan Sufeto Janar na ‘yan sandan Nigeria (IGP), Mrs Elizabeth Kayode Egbetokun, wadda ta jagoranci shugabannin zartaswar kungiyar matan matan ‘yan sanda (POWA) a ziyarar ban girma da suka kai ofishinsa.

InShot 20250115 195118875
Talla

Gwamna Yusuf ya bayyana yadda gwamnatin jihar ke ci gaba da tallafawa ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, musamman ta hanyar samar da kayan aiki da motocin aiki.

Ya kuma jaddada cewa har yanzu harkokin tsaron jihar Kano na daya daga cikin manyan abubuwan da gwamnati ta sa take baiwa muhimman.

“Muna ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma saboda muhimmancin tsaron .

Hukumar tace fina-finai ta haramtawa wani jarumi da wasu mata biyu Film da waka a Kano

“Gwamnatinmu za ta ci gaba da bayar da tallafin da ya kamata domin tabbatar da tsaro a jihar Kano.”

Gwamnan ya yaba da yadda Misis Egbetokun ta himmatu wajen inganta jin dadin jami’an ‘yan sanda da iyalansu.

Gwamna Yusuf ya amince da baiwa filaye da tallafin kudi don gina sakatariyar POWA a Kano.

Da dumi-dumi: NAHCON ta Kayyade Farashin kudin Aikin hajjin 2025

A jawabinta tun da farko, uwargidan Babban Sufeton yan Sandan Nigeria kuma shugaban kungiyar ta POWA, Misis Elizabeth Kayode Egbetokun, ta bayyana cewa sun ziyarci gwamnan ne domin sanar da shi ayyukan POWA a Kano, wadanda suka hada da shirin ba da tallafi da kuma kaddamar da cibiyar lafiya a Panshekara.

Ta yabawa gwamnatin jihar Kano bisa kokarin da take yi na tallafawa mata tare da yin kira da su kara hada kai don tallafawa yan kungiyar ta POWA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...