Wani tsohon ma’aikacin gwamnatin Kano da yayi ritaya ya sadaukar da dukkanin kudin sallamarsa baki daya (Gratuity) don gina masallacin Juma’a a garinsu na Shangu da ke karamar hukumar Rano ta jihar Kano.
Dan fanshon mai suna Alhaji Bello Abdullahi (Sarkin Shangu Murabus) ya sanar da sadaukar da kudin ne ta bakin dansa Alhaji Abdullahi Bell mai garin Shangu, inda ya ce samar da masallacin zai taimakawa al’ummar garin sannan ya zama wata cibiya ta koyar da ilimin addinin Musulunci da tarbiyya ga matasa.

Da yake jawabi a gaban mai martaba Sarkin Rano, Dan fanshon Alhaji Abdullahi Bello ya shaidawa sarkin cewa ya sadaukar da dukkanin kudin da aka bashi wanda suka kai Naira Miliyan 5 domin gina masallacin juma’a a garin na su na Shangu.
” Mun zo gare ka ne ya mai martaba domin na sanar da akai cewa dukkanin kudin da na karba zan gina masallacin juma’a a garinmu, sannan Ina neman izinin sarki da sa albarkarka”.
Hukumar tace fina-finai ta haramtawa wani jarumi da wasu mata biyu Film da waka a Kano
A nasa jawabin mai martaba Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isa Umaru, ya ba kwamitin izinin ci gaba da aikin ginin masallacin.
Sarkin ya yabawa Dan fanshon
Alh. Bello Abdullahi bisa karamci da sadaukarwar da yayi don ci gaban al’umma, ya kuma jaddada muhimmancin al’umma su rika tallafawa don cigaban yankinsu.
Sarkin Rano, Dr. Muhammad Isa Umaru ya ce ” Masarautar a shirye take ta goyi bayan duk wani yunkuri na tabbatar da addinin Musulunci a yankin”.
A wata sanarwa da jami’in yada labaran shiyyar Rano Rabi’u Khalid kura ya aikowa Kadaura24, Ana sa ran al’ummar garin Shangu da kewaye ne za su amfani masallacin Juma’a idan an kammala gina shi.