Dole mu sulhunta Kwankwaso da Ganduje – Abdulmumin Kofa

Date:

Shugaban kwamitin gidaje da muhalli na Majalisar Wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi kira da a gaggauta sulhunta tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje.

Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana hakan a cikin wani sakon murya da ya aikowa Kadaura24 a jiya Alhamis, inda ya bayyana takaddamar da ke tsakanin manyan jiga-jigan siyasar biyu a matsayin abin takaici da kuma illa ga jihar.

Ya kuma bukaci manya masu kishin Kano da su hada hannu wajen sulhunta jagororin siyasar biyu domin ci gaban jihar.

InShot 20250115 195118875
Talla

Da ya ke bayyana nasarorin da su biyun su ka samu, Jibrin ya bayyana cewa shugabannin biyu sun yi fice a aikin gwamnati da kuma samar wa Kano aiyukan more rayuwa.

Za mu sabunta kasuwar Tarauni da ta gyadi-gyadi don inganta kasuwanci – Shugaban K/H Tarauni

Ya danganta yawancin kalubalen siyasar Kano da tsamin dangantakar da ke tsakanin shugabannin biyu, ya na mai kira ga magoya bayansu da su baiwa zaman lafiya fifiko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...