Shugaban karamar hukumar Tarauni, Alhaji Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure tare da hadin Giwar wani kamfanin gine-gine sun bayyana kudurinsa na sabunta kasuwannin ‘Yar Kasuwa Gyadi-Gyadi da kasuwar Tarauni domin bunkasa harkokin kasuwanci da tattalin arzikin yankin.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Tarauni Adamu iliyasu Hotoro ya fitar yace Shugaban sun yi wannan bayani ne yayin ganawarsu da shugabannin kasuwannin tare da mamallakan shaguna a wadannan kasuwanni.

Ahmed Ibrahim Muhammad sekure Ya ce sabunta kasuwannin zai kunshi gyaran shaguna, inganta tsarin tsaro, da samar da yanayin kasuwanci mai kyau ga ‘yan kasuwa da masu zuba jari.
Ahmed Ibrahim Muhammad ya kara da cewa ya dauki wannan mataki ne domin tabbatar da cewa kasuwannin sun dace da zamani.
Shugaban karamar hukumar ya bukaci shugabannin kasuwannin da mamallakan shaguna su kwantar da hankalinsu Babu Wanda zai karbi kudinsu a lokacin Aikin Gina shagunan yace duk Wanda yake da shago Babu Wanda zai rasa shagonsa inda yaroki su ba da hadin kai wajen aiwatar da wannan aiki mai muhimmanci,
Ka rike shawararka ba ma so – Tinubu ga Sarki Sanusi II
Ahmed Ibrahim Muhammad sekure yace karamar hukumar ce zata gaiyato developer da zasu Gina ka su wannin batare da karbar kudin kowanne Mai shagoba tare da tabbatar da cewa duk matakan da za a dauka sun amfanar da kowa.
A jawabinsa a yayin Taron Dan majalisar jiha Mai wakiltar karamar hukumar Tarauni Hon kabiru Dashiru sule ADS ya yi alkawarin cewa Babu wani Mai shago da zai rasa shagonsa inda yace gwamnati za ta ci gaba da daukar matakai da za su bunkasa rayuwar al’umma ta fannoni daban-daban.
A yayin Taron yasami hallartar shugabanin kasuwanin yar kasuwa gyadi gyadi da shugabanin kasuwar Tarauni Alh Haruna Mai Laila store dakuma sarakinan kasuwar inda suka roki shugaban karamar da Dan majalisar dasuyi iyaka kokari wajan ganin Babu wani Dan kasuwa Daya rasa shagonsa inda sukayi Alkawarin bayar da dukkanin hadin da goyen baya domin tabbatar da wannan Aikin na sabunta kasuwanin.