Jami’ar Dutsin-ma ta zata samar da reshenta a birnin Kano – Shugaban Jami’ar

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi.

 

Jami’ar tarayya dake Dutsen-ma a jihar Katsina tasha alwashin bude cibiyar Karatu a cikin birnin Kano domin ba da dama ga matasan dake aiki su sami damar cigaba da karatu ba tare da samun wani tsaiko ba.

Shugaban jami’ar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa da Kungiyar ‘yan jarida ‘yan Asalin karamar hukumar Bichi a rana a Asabar.

Talla

Farfesa Armaya’u ya ce bisa gano cewar nisa da kuma yanayin aiki dake hana wasu musamman masu sha’awar yin karatu a Jami’ar, a yanxu yana shirye shiryen bude cibiyar karatu ta Jama’ar a cikin garin Kano don saukakawa ma’aikata da ‘yan kasuwa.

Inganta Ilimi: Gwamnan Kano zai raba kayan makaranta ga dalibai sama da 789,000

Ya kuma yaba da ziyarar da ‘yan jarida ‘yan Asalin Bichi suka kai masa, inda ya ce hakan zai kara kulla alakar aiki tsakaninsa dasu musamman a bangaren abinda ya shafi cigaba karamar hukumar ta Bichi.

Ya kuma bayyana cewar har yanxu kafafen yada labarai na Radio da Talabijin da Jaridu su ne sahihan hanyoyin samun ingantaccen labarai, sai dai ya ce akwai bukatar yin duba akan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen yada labaran karya da cin zarafin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...