Inganta Ilimi: Gwamnan Kano zai raba kayan makaranta ga dalibai sama da 789,000

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai kaddamar da shirin raba kayan makaranta (Uniform) ga daliban Firamare yan aji 1 a fadin jihar a ranar Litinin 13 ga watan Janairu, 2025 a wani mataki da gwamnatin ta dauka domin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin jihar.

Kimanin dalibai sama da 789,000 maza da mata a makarantun gwamnati 7,092 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar ne ake sa ran za su karbi kayan Masarautar (Uniform)r a karkashin shirin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada Labarai na Kano Com. Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 a lahadi.

Talla

Shiri dai zai inganta tare da baiwa yara damar shiga makarantu da kuma tabbatar da ganin an baiwa kowane yaro dake Kano ingantaccen ilimi, ta yadda za a rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, shirin zai tallafa wa iyayen yara marasa karfi da basa iya daukar dawainiyar ya’yansu, wanda hakan ke kara nuna cewa ilimi shi ne Babban abun da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fi baiwa fifiko.

Rikicin masarautar Kano: Mun gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ta yanke – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta damu da sha’anin ilimi ne domin shi kadai ne zaka baiwa yara su inganta rayuwarsu da ta al’umma idan sun girma.

Taron kaddamar da ba da kayan Masarautar (Uniform) da zai gudana ne da karfe 1:00 na rana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf da kan sa zai kaddamar da shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...