Shugaban gidan Radio jihar Kano Com. Abubakar Adamu Rano ya ce duk yan Kwankwasiyyar da suke komawa wajen Sanata Barau Jibrin rubabbu ne ba abun da zasu iya yi a Siyasance.
“Idan ka lura duk wadanda Barau Jibrin yake cewa ya karba daga NNPP Kwankwasiyya ka kallesu sosai zaka ga ba masu amfani ba ne, wadanda ba za su iya komai ba ne imma lokacin zabe ya zo”. Inji MD Radio
Abubakar Adamu Rano ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa ta musamman da yayi da jaridar Kadaura24.

Ya ce har yanzu Barau Jibrin ya Kasa kutsa kai cikin zaratan matasan Kwankwasiyya, saboda ita Kwankwasiyya dama ta matasa ce ba ta irin rubabbun da Barau Jibrin yake karba ba ce.
” Yanzu kana ganin Barau zai iya shiga cikin matasan schoolers ya ce zai dauki wani, ai ba zai ma fara ba, yanzu ta yaya Barau zai iya karbar su Salisu Yahya Hotoro, Muhammad Kosawa da sauran matanmu na Kwankwasiyya”. Inji Abubakar Rano
Inganta Ilimi: Gwamnan Kano zai raba kayan makaranta ga dalibai sama da 789,000
Abubakar Adamu Rano ya kuma shawarci Sanata Barau Jibrin da ya kula da masu kawo masa mutane da sunan yan Kwankwasiyya ne, saboda kashe mu raba suke yi da wadanda suka kawo don haka sai ya kula.
Ya sha alwashin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai lashe zaben shekara ta 2027 da wawakeken rinjaye.