Rikicin masarautar Kano: Mun gamsu da hukuncin kotun daukaka kara ta yanke – Gwamnatin Kano

Date:

Gwamnatin jihar Kano, ta nuna Jin dadinta da hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke dangane da batun da ya shafi Masarautar Kano na dawo Mai Martaba Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu.

Kwamishinan shari’a na JIhar Kano Barrister Haruna Isah Dediri ya bayyana gamsuwar Lokacin da ya ke ganawa da manema labaru.

Dederi ya ce Hukuncin da kotun daukaka ta yi , ya soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya, ya kuma tabbatar da matakin da gwamnatin Kano ta dauka dangane da nade-nade, mukamai da Kuma gyare-gyare a masarautar Kano.

Talla

” Duk wasu hukunce-hukunce da babbar kotun tarayya ta yi a baya wadanda suka shafi rikicin masarautu a Kano ya zama rusashshe, idan kai la’akari da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a jiya”. Inji Barr. Dederi

Dederi ya ce a madadin gwamnatin jihar Kano suna yabawa bangaren shari’a na kasar nan saboda yadda ya yanke hukuncin ba tare da daukar wani bangare ba, dangane da rikicin masarautu a Kano.

Yanzu-yanzu: Guda cikin kwamishinonin da gwamnan Kano ya sauke ya koma APC

“Da wannan hukuncin za gwamnatin jihar Kano za ta tabbatar da cigaba da aiki kafa da kada da masarautun gargajiya domin ciyar da jihar Kano gaba ta kowacce fuska”. A cewar Kwamishinan shari’a

Daderi ya yi kira da hukumomi da ma’aikatun gwamnati da kamfanoni da Kungiyoyi da daidaikun al’umma da su tabbatar da bin umarnin da kotun daukaka kara ta yi na tabbatar da abun da gwamnatin Kano ta yi akan abun da ya shafi Masarautar Kano.

Ya ce gwamnatin Kano tana kira ga dukkanin bangarorin da abun ya shafa da su Ajiye komai su zo a hada hannu da su don cigaban jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...