Yanzu-yanzu: Guda cikin kwamishinonin da gwamnan Kano ya sauke ya koma APC

Date:

Tsohon kwamishinan ma’aikatar raya karkara ta jihar Kano Alhaji Abbas Sani Abbas ya sauya sheka daga NNPP Kwankwasiyya zuwa Jam’iyyar APC.

” Na bar waccan tafiyar ne saboda abubuwan da ake na rashin adalci ga wadanda muka taho da su”.

Alhaji Abbas Sani Abbas ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibrin da Abdullahi Abbas suka cire masa har hularsa.

Talla

Tsohon kwamishinan ya ce gwamnatin Kano ta gaza taimakawa mutanen da suka sha wahalar kafa ta , ta hanyar amfani da karfinsu da dukiyoyinsu da basirarsu, amma an sami dama an gaza taimaka musu.

” APC dama gida ce a waje na domin da mu aka kafa ta , don haka daga yau na bar Jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya na dawo Jam’iyyar APC”.

Kotun Daukaka Kara ta Bayar da Umarnin Sake Sauraron Shari’ar Masarautar Kano

Ya kuma sha alwashin ba da duk wata gudunmawa da ake bukata domin samun nasarar Jam’iyyar a zabuka masu zuwa.

A nasa jawabin Sanata Barau Jibrin ya yabawa tsohon kwamishinan bisa dawowar da yayi gidansa, inda ya ce dama kaddarace ta sa ya bar ta yanzu kuma ga shi ya dawo.

Ya yi masa Maraba, sannan ya ba da tabbacin jam’iyyar APC za ta cigaba da yin duk mai yiwuwa domin ganin duk dan APC dake Kwankwasiyya ya dawo gidansa na asali.

Kadaura24 ta rawaito Abbas Sani Abbas dai yana cikin kwamishinonin 5 da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke a kwanakin baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...