Kotun daukaka kara da ke Abuja ta bayar da umarnin sake sauraron shari’a kan rikicin masarautar Kano da ya hada da Alhaji Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi.
Kotun daukaka kara, a hukuncin da ta yanke a yau, ta ce ba’a yi wa Aminu Ado Bayero adalci ba saboda yadda wata babbar kotun Kano ta gudanar da shari’a a kansa.

Mai shari’a Mohammed Mustapha wanda ya yanke hukuncin, ya bayyana cewa babbar kotun Kano ba ta yi wa Aminu Ado Bayero adalci ba ta hanyar gudanar da shari’a ba tare da bashi damar bayanin nasa bangaren ba.
Da Dumi-Dumi: Kotun Daukaka Kara ta Yanke Hukuncin akan shari’ar Masarautar Kano
Mai shari’a Mustapha ya ce ya zama wajibi dukkan kotuna su tabbatar da adalci ga kowane bangare ta hanyar ba su dama daidai gwargwado.
Domin haka kotun daukaka kara ta bayar da umarnin a mika karar ga babban alkalin alkalai na jihar Kano domin baiwa wani alkali damar yanke hukunci na adalci cikin gaggawa.
Idan za a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito a watannin baya wata babba kotun jihar kano karkashin jagorancin ta Justice Amina Aliyu ta yanke hukuncin cewa kada Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya sake ayyna kansa a matsayin Sarkin Kano.