Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya roki gwamnatin tarayya da ta rage kudin aikin Hajji duba da irin kalubalen tattalin arziki da ‘yan kasa ke fuskanta .
Gwamnan ya yi wannan roko ne a yayin wani taron da hukumar jin dadin alhazai ta jihar ta shirya domin mayar da kudaden da gwamnatin Saudiyya ta dawo da su ga alhazai sakamakon matsalar wutar lantarki a lokacin gudanar da aikin Hajjin 2023.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 ranar Litinin.

Gwamnan ya kuma yabawa kokarin gwamnatin Saudiyya kan wannan karamci da nuna kulawa ga alhazan Nigeria.
Gwamnan ya yi alkawarin aika wasikar godiya ga gwamnatin Saudiyya ta ofishin jakadancinsu da ke jihar Kano.
Ya kuma nuna godiya ga hukumar alhazai ta kasa NAHCON bisa tsantseni da biyan kudi akan lokaci.
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya rabawa sabbin kwamishinoni ma’aikatu
Gwamna Yusuf ya bayyana jin dadinsa kan kokarin hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano bisa gudanar da aikin Hajji cikin nasara wanda har aka yaba mata a kasa baki daya.
Gwamnan ya bayyana cewa ya ziyarci kasar Saudiyya a makonnin da suka gabata domin gudanar da ibadar Umara sannan kuma ya kaddamar da shirye-shiryen zuwa aikin Hajji na bana ta hanyar gano wuraren da ya kamata gwamnatin jihar ta kamawa maniyatanta.
A nasa jawabin mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda shi ne shugaban tawagar alhazan Kano na shekarar 2024 ya yaba da irin tallafin da gwamna Yusuf ya baiwa alhazai kafin da lokacin da kuma bayan kammala aikin hajji.
Tun da farko, Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Laminu Rabiu Danbaffa ya ce jimillar kudaden da aka mayar wa jihar ta hannun hukumar alhazai ta kasa domin rabawa Alhazan da suka yi aikin hajjin 2023 sun kai Naira miliyan 375.