Ana barazana ga rayuwata – Peter Obi

Date:

Ɗantakarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana saboda sukar gwmnatin Shugaban Ƙasa Tinubu da ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara.

A saƙon nasa na sabuwar shekarar, Obi ya bayyana cewa Najeriya na fama da taɓarɓarewar tattalin arziki da rashin tsaro da rashin ingantaccen kiwon lafiya.

Talla

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya ce, “shin na wuce iyaka? na yi wannan tambayar ce saboda ana yi wa rayuwata da ta iyalina barazana saboda jawabin da na yi na sabuwar shekara. Bayan barazanar kuma, wani mai suna Mr Felix Morka ya zarge ni da wuce iyaka, sannan ya yi barazanar zan ɗanɗana kuɗata,” in ji shi.

Obi ya ƙara da cewa idan har da gaske ya karya doka, a nuna masa, inda ya ƙara da cewa, “amma ba zan daina faɗin gaskiya ba, musamman a wannan lokacin da ƙasarmu ke ƙara shida cikin ruɗu.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...