Za mu hada hannu da gwamnatin Kano don tallafawa makarantar da muka gama – Kungiyar DATSOSA aji na 2000

Date:

Daga Shehu Husaini Ahmad Getso

 

Kungiyar tsofaffin Daliban kwalejin Kimiyya ta Dawakin Tofa aji na shekara ta dubu biyu (2000) ta jaddada kudirinta na hada hannu da gwamnatin jihar Kano domin farfado da martabar kwalejin tayadda zatayi gogayya da cigaban wannan zamani.

Shugaban kungiyar Comerade Dahiru Ibrahim Malami ya bayyana hakan lokacin da yake jawabin maraba ga ‘ya’yan kungiyar a taron karshen shekara da kungiyar ta gudanar na shekarar 2024 da mukayi ban-kwana da ita.

Talla

Comerade Dahiru Malami yace taken taron na wannan karo shine”Duba yuwuwar farfado da martabar kwalejin Kimiyya ta Dawakin Tofa kamar yadda aka Santa a baya koma fiye da yadda take a baya”.

Ya ce a iya nazarin da kungiyar ta yi wata da watanni,kungiyar ta lura kwalejin a yanzu haka tana fuskantar koma baya a bangaren ababen more rayuwa musamman kuma a dakunan kwanan dalibai,wuraren cin abinci,wuraren wasannin motsa jiki da makamantansu.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya rabawa sabbin kwamishinoni ma’aikatu

Yace yaji dadin yadda Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamitin ko-ta-kwana a bangaren ilimi,Wanda hakan zai taimaka wajen cigaban ilimi a jihar Kano baki daya,a saboda haka zasu duba yuwuwar hada hannu da Gwamnatin jihar ta Kano domin samun nasarar wannan yunkuri a kwalejin Kimiyya ta Dawakin Tofa.

A karshe Dahiru Ibrahim Malami yace a yanzu kungiyar na shirye-shiryen gudanar da wani kasaitaccen biki na cikar ‘ya’yan kungiyar shekaru 25 da kammala karatu a kwalejin,taron dashi suke fatan ya taimaka wajen haifar da sauyi mai cikakkiyyar ma’ana a kwalejin baki daya.

 

Dayake jawabi, daya daga cikin jagororin kungiyar ta DATSOSA CLASS-2000,Dr Andulwahab Kabir na Asibitin kwararru Murtala Mohd dake Kano ya yabawa ‘ya’yan kungiyar bisa namijin kokarinsu ba gajiyawa wajen tallafawa marayu ko Iyalan wasu daga cikin “ya’yan kungiyar da suka rigamu gidan gaskiya.

Da dumi-dumi: Kwamishina a Gwamnatin Kano ya ajiye aiki

Ya ce an dauki shekaru da dama ana aiwatar wannan tsarin, wanda kuma yake taimakawa kwarai wajen samun cigaban su marayun da abin ya shafa a zarafofin neman ilimi da hanyoyin dogaro dakai.

Daganan Dr Kabir sai ya bukaci ‘Ya’yan kungiyar da kadda su gajiya wajen tallafawa wadanda suka cancanci a nuna masu tausayawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...