Alhaji Shawall Barau Jibrin, Shugaban Gidauniyar Shawall Barau I Jibrin, kuma Shugaban Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Barau Academy, ya lashe lambar-girma ta Ingantaccen Jagoranci da Tallafawa Al’umma ta 2024, wato “2024 Best Award of Excellence in Leadership and Philanthropy.”
Wannan lambar-girma, wacce MARYORKINGS AGENCY GROUP ta gabatar, wata manuniya ce ga irin gudunmawar da Shawall ya bayar wajen ci gaban matasa, ayyukan jin-ƙai, da hidimar al’umma a Arewacin Najeriya.
Shawall, mutum mai taimakon al’umma da hangen-nesa, wanda ya fito daga Jihar Kano, ya yi tasiri mai girma ga rayuwar al’umma ta hanyar shirye-shirye daban-daban na taimakon al’umma.

Manyan nasarorinsa sun haɗa da daukar nauyin karatu, ciyar da marayu sama da 10,000 a lokacin watan Ramadan, rabon abinci da tufafi ga iyayen marayu, da aiyukan samar da ababen more rayuwa da suka inganta rayuwar al’umma a Arewacin Najeriya.
Da dumi-dumi: Dillalan mai sun bayyana Sabon farashin man fetur a Nigeria
Wannan kyauta, wata jinjina ce ga jajircewar Alhaji Shawall wajen inganta rayuwar matasan Arewa da tallafa wa marasa galihu. Har ila yau, ta haskaka rawar da ya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya ta hanyar samar da ayyukan yi, karfafa wa matasa gwiwa, da shirye-shiryen rage talauci.
MARYORKINGS AGENCY GROUP ta bayyana nasarorin Alhaji Shawall a matsayin abin koyi, tana mai jaddada cewa aikinsa ya kafa ma’auni mai girma ga jagoranci da ayyukan tallafi.
Bayan Shawall ya zarta sauran wadanda aka zaba, ya kuma zama wanda ya dace da wannan babbar kyauta, lamarin da ya tabbatar da kyakkyawan hali da ya bari na sauyin rayuwa mai kyau.
Wannan bikin bada kyautukan ya fito da irin rawar da masu sana’o’i, ƴan kasuwa da masu nishadantarwa ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da taimakon garuruwansu da yankunan su.