SEDSAC ta Yabawa Gwamnan Kano Bisa Nadin Wayya da Iro-ma’aji a Matsayin Kwamishinoni

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Kungiyar rajin kare dimokaradiyya da muradan al’umma wato SEDSAC ta yabawa gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa sanya Yan kungiyoyin farar hula cikin kunshin majalisar zartarwarsa.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Gwamnan jihar kano ya nada Amb. Ibrahim Abdullahi Wayya da

” Wannan matakin da gwamnan Kano ya dauka ya nuna cewa yana son tafiya da yan gwagwarmaya wanda suka dade suna taimakawa al’umma, Kuma hakan zai karawa gwamnatin kima a idanun duniya”.

Talla

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban daraktan kungiyar SEDSAC Kwamaret Hamisu Umar Kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma aka aikowa kadaura24.

Shawall Barau Jibrin ya zama Gwarzon Shekarar 2024 Saboda taimakon al’umma

Sanarwar ta ce nada Amb. Ibrahim Wayya da Iro-ma’aji a matsayin kwamishinoni ba kawai abun yabo ba ne ga gwamnan, ya nuna yadda yake kishin dimokaradiyya da son cigaban Kano saboda ya zabo masu gaskiya da kwarewa ya sanyasu cikin gwamnatinsa.

Kungiyar ta SEDSAC ta taya yan gwagwarmayar murnar samun wannan mukami tare da bukatar su da su kara zage damtse don nuna kwarewa akan aikinsu don gudun kada su baiwa gwamna da sauran kungiyoyin farar hula Kunya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...