Dillalan mai da ke siyan man fetur daga Kamfanin matatar Dangote , sun rage farashin man fetur da kashi 11.8%, daga N1,060 zuwa N939.50 kowace lita.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Matatar mai ta Ɗangote ta rage farashin man fetur saboda bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.

A jiya, dillan mai suna sayar da man fetur a kan N1,060 kowace lita, bisa binciken Vanguard a Legas da kewayenta.
Amma a yau, binciken da Vanguard ta yi ya nuna cewa MRS, wani babban kamfani mai sayar da man fetur, da wasu sun rage farashin .
Da aka tuntubi shugaban MRS, Alhaji Sayyu Idris Dantata, ya ki yin tsokaci, amma ziyara zuwa tashar man fetur ta kamfanin a Ojota, Legas, ta tabbatar da cewa MRS ta fara sayar da man fetur a kan N939.50 kowace lita.
Kamfanin Dangote ya rage farashin man fetur na ex-pump zuwa N899.50 kowace lita, daga N970 kowace lita.