Daga Jamila Umar Musa
Cin zarafi ga mata da ‘yan mata shi ne matsala mai girma da ke damun duniya. Shi ne keta haddi na ‘yancin dan Adam, barazana ga lafiyar jama’a, da kuma barazana ga ci gaban tattalin arziki.
A Najeriya, musamman a jihar Zamfara, cin zarafi ga mata da ‘yan mata shi ne damuwa mai girma. Mata da ‘yan mata da dama ana zarginsu zuwa ga zarafin jiki, tunani, da jima’i, wanda galibi yake da sakamako marasa kyau.
A kan ware kwanaki 16 daga 25 ga watan nuwamban ko wace shekara zuwa 10 ga watan December domin kara wayar da kan alumma akan ilolin cin zarafin jinsi , abubuwan da yake haifarwa a cikin alumma da kuma yadda daidaikun alumma ya kamata su kare kansu daga fadawa ciki. Hakama idan sun fada ya yakamata suyi.
Jahar zamfara ma na daya daga cikin jahohin da suka gudanar da wannan rana ta cin zarafin jinsi mussamman ga mata dama kananan yara.
Yayinda itama gwamnatin jahar a nata bangaren ta sha alwashin kawo karshen wannan matsalar mussamman yayinda yafi kamari a yankunan karkara.
A nata kokarin don ganin an kara wayar da kan al’umma akan daidaiton jinsi da kuma cin zarafin mata dama kananan yara, itama uwargidan gwamnan jihar zamfara Hajiya Huriya Dauda lawal ta kaddamar da nata tattakin da kuma kokarin ziyartar wasu kananan hukumomi domin ganin ta gana dasu da kuma bayar da kayan amfani zuwa gare su. Ta kuma kammala Kanfen dinta da ta soma na kwanaki 16 a kokarinta na yaki da cin zarafin mata da maza, tare da gudanar da Wasu muhimman matakai na gina al’umma da kuma kauda tashe-tashen hankula a Zamfara.
Ta kuma halarci taron shekara-shekara na kungiyar matan gwamnonin Najeriya karo na 5 da aka gudanar a Abuja, inda aka jaddada muhimmancin kalubalantar munanan ayyuka da karfafa dokar kariya ga mata da yara.

A bangaren malaman addinima su kan kara kira da kuma fatawa akan muhimmancin da macce take da shi a cikin al’umma, Wanda gudunmuwar da suke bada wa a wannan haujin ya sa a bana a jihar Zamfara an samu sauyi da kuma raguwar wadanda kaddarar cin zarafi ta same su.
Har wayau suma sarakunan gargajiya suna taka muhimmuyar rawa sosai wajan ganin an kara wayar da kan al’umma mussamman na karkara , wajan ganin cewa idan hakan ta same su su fito su yi magana don cimma abinda ake bukata,
A cewar Sarkin katsinan Gusau Dr Ibrahim Bello.

” rashin magana da mutane basu yi yana kara nakasu a rayuwar su da ma lafiyar su. A don haka muke kokarin ganin cewa mun cigaba akan kira da kuma wayar da kan alumma akan kawo karshan cin zarafi mussamman ga mata da kananan yara”.
Hakama Abubuwan da ke haifar da cin zarafi ga mata da ‘yan mata sune na gajeren kalmomi.
Sun hada da ra’ayoyin al’umma da kaidodin da ke ci gaba da kawar da matsayin mata, rashin ilimi da damar cinikin tattalin arziki, da kuma kudirin doka da manufofin da ke kare hakkin mata.
A jihar Zamfara, akwai kungiyoyi da dama da ke aiki don kawo karshen cin zarafi ga mata da ‘yan mata. Wadanda suka hada da Kungiyar intersos da ke da offishinsu a baban birnin jahar Gusau
– Ma’aikatar Mata da Harkokin Yara ta Jihar Zamfara, wacce ke bayar da hidimam na tallafi ga wa’anda suka tsira daga zarafi da kuma aiki don kare hakkin mata – Kungiyar Kasa ta Mata ta Najeriya, wacce ke bayar da taimako na kudi ga kungiyoyin mata da kungiyoyin da ke aiki don kawo karshen cin zarafi ga mata da ‘yan mata Da ma hidimam na tallafi ga wa’anda suka tsira daga cin zarafi.
Hakama kungiyoyi da dama suna kokarin wajan cewa sun bunkasa wajan ganin sun kara wayar da kan alumma domin ganin matsalar da cin zarafi ke haifarwa mussamman ga lafiya Dan Adam da kuma lafiyar kwakwalwa .
shugaban hadadiyar kungiyoyi masu fafutukar yaki da cin zarafin jinsi na jahar zamfara.
Dr Ahmad Hashim ya bayyana cewa

“Muna kokarin cewa wata shekara a samu ragin kididigar wainda suka fuskanci cin zarafi a don haka zamu cigaba da yekuwa ta kafafen watsa labarai don ganin an cimma abinda aka sa a gaba.”
“Cin zarafin mata dama kananan yara ya zama abin damuwa da kuma dubawa a cikin alumma. “Mussamman yanda taken wannan shekara ya zama kawo karshen cin zarafin mata dama kananan yara gaba daya.”
Da Karshe, domin kawo karshen cin zarafi ga mata da ‘yan mata akwai bukatar gwamnati , kungiyoyi , dama daidaikun jama’a, su hada hannun da kuma nuna kishi Domin aiki tare Don karfafa dokoki da kuma manufofin dake kare hakkin mata da ma na kananan yara wajan wayar da kan al’umma game da illolin cin zarafi ga mata da ‘yan mata.
Shirye-shirye zuwa ga al’umma don wayar da kan mata da maza game da cin zarafi.
-Kafa kungiyoyin tallafi ga wa’anda suka tsira daga cin zarafi.
-Gyaran dokoki da kuma aiwatar da su don Bayar da ilimi da damar cinikin tattalin arziki don karfafawa mata da ‘yan mata
– Bayar da na tallafi ga wa’anda suka tsira daga cin zarafi, gami da basu shawarwari, da kulawa da lafiyar su , da taimako na shari’a.
Mata iyayen mu ne mu dakatar da cin zarafin jinsi mussamman ga mata dama Yan mata.