Ministan Man fetur ya Yabawa Kamfanin NNPLC Bisa Aiwatar da Manufofin Tinubu

Date:

 

Karamin ministan albarkatun man fetur da Iskar Gas Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo ya yabawa kamfanin NNPC bisa nasarar aiwatar da manufofin shugaban kasa ta hanyar samar da ayyuka masu tasiri ga ‘yan kasa.

Karamin Ministan ya yaba tare Jinjina a wata ziyarar aiki da ya kai Cibiyar Aikin Samar da wutar lantarki dake Maiduguri.

Wannan katafaren aiki guda ne cikin ire-iren ayyuka samar da wutar lantarki na gaggawa dake Maiduguri (MEPP) wanda Shugaban kasa Bola Tinubu ta kaddamar domin amfanar ‘yan kasa.

Talla

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a cibiyar samar da lantarkin ranar Asabar, 14 ga watan Disamba, 2024.

Ministan wanda ya samu rakiyar shugaban rukunin kamfanin NNPC Ltd., Mele Kolo Kyari, da mataimakin shugaban kasa, da sauran masu ruwa da tsaki na kamfanin NNPC.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya baiwa Sani Danja da wasu mutane Mukamai

Ita dai cibiyar samar da lantarkin MEPP wani aikin hadakar wutar lantarki ne mai karfin megawatt 50 da aka kaddamar a ranar 2 ga Maris, 2023.

Rahotonni sun ce tuni an riga an kammala aikin 32MW na aikin kuma tuni ya fara aiki, yayin da sauran Megawatt 18MW zai fara aiki cikin shekarar 2025 dake karatowa.

Ga hotunan yadda ziyarar ta kasance:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related