Na Yi Nadamar Abun da Na Yiwa Marigayi Nafi’u – Jarumar TikTok Babiana

Date:

Fitacciyar ’yar Tiktok Hafsat Babiana ta yi tattaki har Jihar Bauchi daga Kano domin neman yafiyar iyayen Nafi’u wanda ake zargin Hafsat Chuchu ta kashe a Kano.

‘Yar Tiktok ɗin sanye da hijabinta har ƙasa ta bayyana a soshiyal midiya tana bayyana nadamarta kan munanan maganganun da ta yi a kan marigayin duk kuwa da cewa tana sane da cewa ba gaskiya ba ne.

A shekarar da ta gabata ne dai aka fara tuhumar Hafsat Chuchu da laifin kashe yaron mijinta Nafi’u, bayan saɓani ya shiga tsakaninsu.

Talla

Har yanzu dai batun na gaban kotu ba a kammala shari’a ba.

Tun a wancan lokacin mutane da dama ke tofa albarkacin bakinsu kan lamarin, musamman kan haƙiƙanin alaƙar da ke tsakanin Chuchu da Nafi’u.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya baiwa Sani Danja da wasu mutane Mukamai

Kan hakan ne Babianan ta ce da ita da ma duk wanda ya san yana cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu ba tare da ƙwaƙƙwarar shaida ba, su nemi yafiyar iyayen marigayin.

Na yi tattaki daga Kano har Bauchi domin nema yafiyar iyayen Nafi’u saboda abubuwan da suke faruwa kwana biyu a rayuwata.

“Na taɓa yin ‘update’ akan wanda aka kashe, wanda kullum idan na kwanta ina tunanin abin da na yi masa bai dace ba a rayuwa.

“Na yi cigiya sau da dama ko da waɗanda suka san danginsa ban samu ba sai daga baya.

“Na duba na ga an kashe ɗansu kuma ana ta bin sa da muggan kalamai duk da babu wanda ya san gaskiyar abin da ya faru sai Allah.

Sanata Kawu Sumaila ya Bayyana Dalilin Alakarsa da Jam’iyyar APC a Yanzu

“Amma dukkanmu ba mu yi wa iyayensa adalci ba, a matsayinmu na mutanen da mu ma idan an yi mana ba za mu ji daɗi ba. Amma haka duka muka rufe ido muka dinga yaɗa jita-jita da sharri muka yi wa mamaci.

“To ni dai ban kyauta ba kuma na fito na ce ni ba ni da masaniya a kan rayuwarsa. Iya abin da idona ya gani na je na samu iyayensa da shi. Ba su zage ni ba, ba su ci min mutunci ba, ba kuma su yi min Allah wadai ba. Hasali ma sun karɓe ni a matsayin ’yarsu.”

A ƙarshe ta ce tana fatan za a yi wa iyayen na Nafi’u adalci a shari’ar da ake fafatawa a kotu, domin ita ce kaɗai hanyar da za a kwantar musu da hankali

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...