Sanatan Kano ta Kudu Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya bayyana cewa jagoran tafiyar Kwankwasiyya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya kulla alakar dake tsakaninsu da jam’iyyar APC.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito mabiyan Kwankwasiyya suna ta sukar Kawu Sumaila tare da zargin cewa yana da alaka da yan Jam’iyyar APC saboda yana so ya bar tafiyar su ta Kwankwasiyya a jam’iyyarsu ta NNPP.
A wata hira da yayi da manema labarai a Kano, Sanata Kawu Sumaila yace akan Kujerar Abba Gida Gida, sunje duk inda ake zuwa don neman ayi musu adalci.

Yace Kwankwaso ne ya kira su (yan majalisar tarayya) ya ja hankalinsu akan su hadu waje guda domin tunkarar duk wanda ya kamata domin a tabbatar da Kujerar gwamnan Kano.
“Jagora Rabi’u Musa Kwankwaso ne ya kirawo mu gidansa , ya yi mana magana ta jagora da mabiya ya ce ya zama dole mu dunkule wurin guda mu je duk inda za mu don ganin ba a kwacewa Abba Kabir Yusuf kurarsa ta gwamnan jihar Kano ba”. Inji Sen. Kawu
Gwamnatin Kano ta tallafawa mata 200 musu lalurar yoyon fitari da Jarin dogaro da kai
Sanata Kawu Sumaila”ya ce ni da Abdullahi Sani Rogo da Abdulmumini Jibrin Kofa Mun ta shi mun nuna masa matsalar shiga cikin maganar amma ya dage sai Mun yi abun da ya fada, sannan ya kawo mana dalilai da hujjojin da har suka sanya muka gamsu da abun da ya zo da shi”.
Sai dai yace ko kusa ko alama, shi a saninsa jam’iyyar NNPP bata shirya wani magudin zabe a lokacin babban zaben shekarar 2023 ba, domin tare dashi aka yi komai na yakin neman