Gwamnatin Kano ta tallafawa mata 200 musu lalurar yoyon fitari da Jarin dogaro da kai

Date:

Daga Rabi’u Usman

 

Kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara da masu bukata ta musamman ta jihar kano Haj Aisha Lawan Saji Rano ta bayar da tallafin jari na Naira Dubu 30 ga mata masu lalurar yoyon fitari su 200 domin gudanar da sana’o’in dogaro da kai da inganta rayuwar su.

Hajiya Aisha Lawan ta ce ta bayar da tallafin ne a wani bangare na cigaba da ranar yaki da cin zarafin mata da kananan yara ta duniya.

An dai gudana da taron ne a harabar inda aka ajiye masu yoyon fitsari a kwaryar birnin kano, inda Gidauniyar Fistula ta koyar da mata 200 sana’o’in dogaro da kai domin samun damar taimakawa ‘yayan su da inganta rayuwar su musamman wadanda suke kula da su.

Talla

Kwamishiniyar ta yi kira ga mata dasu dinga zuwa yin awo asibiti domin tabbatar da lafiyar su kafin haihuwa domin gudun kamuwa da larurar yoyon fitsari.

Aisha Rano dai tana daga cikin kwamishinonin da suka samu sauyin ma’aikatu a jihar kano, Wanda gwamnatin kano ta mayar da ita ma’aikatar kula da yawon Bude idanu da raya Al’adu ta jihar kano.

Shugaban karamar hukuma a Kano ya kwace wata makarantar Islamiyya saboda ta gayyaci Sarkin Aminu Ado Bayero

Ta yi kira ga wadanda suka rabauta da tallafin da yi amfani da shi ta hanyar da ta dace har ma ta karfafa musu gwiwa wajen zuwa asibiti domin tabbatar da koshin lafiyar su.

Shugabar dake kula da gidan masu yoyon fitsari ta jihar kano Aisha Sani kurawa ta mika godiya ga gwamnatin kano musamman ma’aikatar mata kananan yara da masu bukata ta musamman a madadin mutanen da suka amfana da tallafin kudin da za su ja jari domin dogaro da kawunan su, tana mai cewar wannan shi ne karo na farko da aka ta6a baiwa masu larurar yoyon fitsari tallafi a jihar kano.

A nasu bangaren wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun nuna jin dadin su tare da alwashin yin amfani da tallafin kudin wajen yin sana’oin da suka koya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...