Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Shugaban karamar hukumar Nasarawa Amb. Imam Yusuf ya Kwace wata makarantar Islamiyya saboda ta sanya hoton Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero a cikin kalandar makarantar tare da gayyatar Sarkin.
” Ba za mu lamunci wata makaranta ta sanya hoton wani wanda ba Sarki ba a cikin kalandar, saboda yin hakan neman kawo cikas ne ga zaman lafiyar da muke da shi a Nasarawa”.
Kadaura24 ta rawaito cewa Amb. Imam Yusuf ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai a Ofishinsa.

” A kawai wata makarantar Islamiyya mai suna Ubaiyu Bn Ka’ab dake unguwar gama a karamar hukumar Nasarawa da ta dauki hoton wani wanda ba shi bane sarki Kano a cikin kalandarta tare kuma da gayyatarsa wannan abun da suka yi ya saba dokarmu”. Inji ogan Boye
Shugaban karamar hukumar Nasarawa ya ce su a saninsu khalifa Muhd Sanusi II shi ne Sarkin Kano, don haka ba za su lamunci wani ko wata su rika kiran wani Sarkin Kano ba , alhakin kuma ba shi ba ne.
Majalisar Shura ta Darikar Tijjaniyya ta yabawa Gwamnan Kano bisa Nadin Habib Dan almajiri
Ya ce ya Kwace makarantar daga wannan rana ya mayar da makarantar karkashin kulawar Sakataren ilimi na karamar hukumar tare da rushe duk shugabannin makarantar.
” Daga yau Ina ba da umarnin kada wata makaranta ko hukuma ta gwamanti ko mai zaman kanta ta sake sanya hoton wani Sarki wanda ba Sarki Sanusi na II ba”.