Dalilin da ya sa dole kwararru su rika kula da gine-gine don tabbatar da ingancinsa – Kakakin Abbas

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Shugaban majalisar wakilai ta Nigeriya Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ya yi kira da a rika karfafa cibiyoyin gwamnati, musamman wadanda suke kula da ka’idoji da tsare-tsaren gine-gine don cigaban ƙasa.

Kakakin majalisar ya yi wannan kiran ne ranar talata a ofishinsa da ke Abuja, a lokacin da majalisar koli ta Cibiyar masu kula da Gudanar da Ayyuka ta Najeriya (CIPMN) ta ba shi lambar yabo ta girmamawa ta Cibiyar.

Shugaban majalisar Abbas wanda ya danganta rugujewar gine-gine da sauran ababen more rayuwa a sassa daban-daban na Nigeria da gazawar hukumomin da ke da alhakin tabbatar da ingancin aiyukan .

Talla

Ya bayyana cewa tun da ya zama dan cibiyar CIPN, zai shiga yakin neman ganin ana gudanar da ayyuka yadda ya kamata a kasar nan.

Ya ce: “Hakika Cibiyarku tana da dabaru sosai. Idan da mu – ’yan Najeriya – za mu kyale ta ta yi aiki yadda ya kamata, za a iya gyara abubuwa da yawa. Mun ji labarin rugujewar gadoji, gidaje, da abubuwa iri-iri a Najeriya. Na yi imani da an baiwa cibiyoyi irin na ku na kwararrun damar kula da aiyukan da ba tsinci kai cikin halin da ake ba”.

Yadda Mai aikin shara a Kano ya Mayar da Naira Miliyan 40 da ya tsinta

“Ina ganin tun da na zaman mamban a wannan cibiya mai albarka, zan kasance daya daga cikin jakadunta da za su nemowa cibiya damar gudanar da ayyukanta yadda ya dace, wanda a karshen hakan zai kai Nijeriya ga wani matsayi mai girma.

Shugaban majalisar, wanda ya ce, “yau rana ce ta farin ciki a gare ni da kuma majalisar wakilan Nigeriya, saboda wannan karramawa da lambar yabo da aka ba mu, duba da irin gudunmawar da muka bayar a kokarinmu na gina kasa,” ya kara da cewa, “Ina so in sanar da ku cewa na amince na shiga wannan cibiya mai albarka.”

Gwamnatin Kano ba zata saurarawa masu sayar da filaye ba bisa ka’ida ba – Kwamitin karta kwana

Ya kara da cewa da alhakin zama mai sa ido, mai wayar da kan jama’a, mai aiwatar da doka da ke jagorantar manajojin ayyuka, “dukkan wadannan abubuwa, ina mai tabbatar muku da cewa na amince za mu gina kasa daya dunkulalliyar Nijeriya inda dokoki da ka’idoji za su zama namu. kalmar tsaro.”

Shugaban majalisar gudanarwa ta Cibiyar CIPMN, Dr. Jamilu Isa Yankwashi wanda ya jagoranci tawagar ya yaba da salon jagorancin kakakin majalisar Abbas da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban kasa.

Ya ce tun da ya zama shugaban majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya nuna kansa tare da nuna jajircewarsa wajen gina kasa, inda ya bayyana shugaban majalisar a matsayin shugaba mai kishin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...