Kungiyar DHS International ta yi Aikin Dubawa da Rabawa Marasa Lafiya Magani Kyauta a Kano

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

Mataimakin Shugaban Kasa Senator Kashim Shettima GCON ya kaddamar da duba marasa lafiya tare basu magunguna kyauta da bada taimako abinci ga Jama’a a Kwaleji Ilimi ta Tarrayya dake Bichi wanda ya dauki nauyi ta Kungiyar DHS International & Project Rescue Nigeria wanda ya gudana a Babban dakin taro na Kwalejin.

Mataimakin Shugaban Kasa Wanda Sanata Abba Aji ya wakilta, ya ce gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tunibu zata cigaba da ingarta rayuwa Jama’a.

Sanata Abba Aji ya kira da masu hannu da shuni dasu taimaka Jama’a.

Talla

A jawabinsa Shugaban Kungiyar DHS International & Project Rescue Nigeria team na Kasa Amb. Dr Ibrahim Bala Aboki ya ce a matsayisa na Shugaban Kungiyar sun zabi a fara gabatar da shirin a garin Bichi a matsayinsa na tsohon dalibi na Kwalejin ta Bichi duba da irin gudumarwa da aka basu a rayuwa yayi da suke karatu a Kwaleji.

Yace sun zabi Cututtukan da suka fi damun Jama’a Kamar Olcer, ciwon suga, zabarbin cizon sauro da sauransu domin ba da ganinsu.

Ya kara da cewa Kungiyar zata cigaba da bada wannan tallafi karkashin Jagoranci uban kungiyar na Kasa Mataimakin Shugaban Kasa Senator Kashim Shettima GCON.

Shi ma a nashi Jawabin Shugaban Kwaleji ta FCE Bichi Dr Bashir Sabo Abubakar ya godewa Mataimakin Shugaban Kasa Senator Kashim Shettima GCON tare da Kungiyar DHS International bisa bada wannan tallafi ga Jama’a sama da dari biyar 500.

Taro ya sami halatar Dan uwar ga Mataimakin Shugaban Alh Usman Shettima, Mallam Musa Aliyu Jahun (Magajin Mallam), Alh Yakubu Ibrahim tagaho (Sarkin noman Gaya), Alh Ibrahim Haruna BBY, Alh Audu Ladiyo da Kuma Alh Danladi Wadari da sauran Jama’a da dama.

Ga hotunan yadda taron ya Kasance

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...