Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Kwamitin karya Kwana da gwamnatin jihar kano ta kafa domin yaki da masu yin gine-gine ba bisa ka’ida ba ya sha alwashin daukar matakan Shari’a akan duk wadanda aka samu da sayar da filayen awon igiya a unguwar Katsinawa dake bachirawa a karamar hukumar Ungoggo.
” Ma’aikatar filaye da tsare-tsare ta jihar kano ta kudirci aniyar yaki da duk mutanen da suke sayar da filaye a jihar kano ba bisa ka’ida ba, tare da rushe duk wasu gine-gine da aka yi ko ake yi ba bisa ka’ida ba”.
Sakataren kwamitin karta kwanan Hamidu Sidi Ali ne ya bayyana hakan lokacin kwamitin ya ziyarci unguwar , a cigaba da rangadin da kwamitin ke yi don kawar da gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba.

Ya ce wasu marasa kishin jihar kano ne suka yanka filaye a unguwar ta Katsinawa dake Bachirawa ba tare da sanin gwamnati ba, kuma suke sayarwa al’umma.
” Muna kira ga al’ummar jihar Kano da su guji siyan Irin wadancan filaye da ake yankasu ba bisa ka’ida ba, su kuma masu sayarwar muna sanar da su cewa ba zamu saurara musu ba, muddin ba daina cutar al’umma ba ta hanyar sayar musu da filaye Barkatai”. Inji Hamidu Sidi Ali
Kotu ta ki bayar da belin Yahya Bello
Hamidu Sidi Ali wanda kuma shi ne daraktan mulki da gudanarwa na ma’aikatar filaye ta jihar kano ya ce ma’aikatar karkashin jagorancin kwamishinanta Abduljabbar Umar ta fito da sabbin tsare-tsare domin saukakawa al’umma don su sabunta takardun gidaje da filayensu.