Rundunar yan Sanda ta kasa reshen jihar Kano, ta tabbatar da cewa mutane 2 sun rasa rayukansu, sakamakon fadan daba da ake zargin wasu matasa daga unguwannin , Zango da kuma Kofar Mata sun yi tun a jiya lahadi.
Mai magana da yawun Rundunar a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da manema labarin, a shelkwatar Rundunar dake unguwar Bompai Kano.
SP Abdullahi Kiyawa, ya ce tun a ranar Lahadi, suka samu kiraye-kiraye daga unguwar kofar Mata, a daidai lokacin da aka tashi daga wasa a filin wasa na Sani Abacha Stadium, Inda wasu matasa suka rinka yin fadace-fadacen daba Tsakanin Unguwa da Unguwa.

” Bisa rahotannin da mu ka samu an ce mana fadan Daba ne Tsakanin unguwar Zango da kuma Kofar Mata” cewar SP Abdullahi Haruna Kiyawa “.
Kiyawa ya kara da cewa bayan Samun rahotannin marasa Dadi kwamishinan yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya Tura dakarun Yan Sanda da gaggawa wajen da lamarin ya Faru , kuma sun Samun rahotan Mutuwar mutane 2.
Dalilan da Suka Sanya Darajar Naira Nigeria ta Daga – Masana
Rundunar ta ce yanzu haka an dukufa wajen gudanar da bincike don ganin duk Wanda yake da Hannu akan fadace-fadacen dabar, ya zo don ya fuskanci hukunci.
Kiyawa ya ce ko a wannan rana ta lahadi sai da Kwamishinan yan sandan jihar Kano CP Salman Dogo sai da ya je unguwanni da lamarin ke faruwa domin tabbatar da komai ya koma dai-dai a yankin.
A karshe Rundunar taja hankalin al’umma, musamman wajen taimaka wa jami’an Yan Sandan da bayanan sirri, tunda dai wadanda suke aikata laifukan Yan unguwane.
Idon Gari.