Hukumomi a Najeriya sun ce kuɗin ƙasar, naira na ƙara daraja a baya-bayan nan.
Wannan ne karon farko tun daga watan Mayun 2024 da naira ta shafe kwana biyar a jere tana ƙara daraja a kasuwar canji.
Wasu da dama a ƙasar na alaƙanta samun tagomashin kuɗin Najeriya da wasu sabbin tsare-tsaren da Babban bankin ƙasar (CBN) ya aiwatar, musamman a fannin hada-hadar kuɗi ta intanet, mai suna Electronic Foreign Exchange Matching System (EFEMS), a makon da ya gabata.

Tun bayan sauya manufofin gwamnatin Najeriya a harkar kuɗi jim kaɗan bayan zuwan shugaban ƙasar Bola Tinubu a 2023, darajar naira ta riƙa karyewa, lamarin da ya ƙara jefa tattalin arziƙin ƙasar cikin matsi sanadiyyar tashin farashin kayan masarufi.
A lokacin da Bola Tinubu ya karɓi mulki, cikin watan Mayun 2023, ana sayen dalar Amurka ne kan kimanin naira 750, sai dai dalar ta haura naira 1,000 ya zuwa farkon shekara ta 2024.
Za mu biya kudaden daliban Kano da Ganduje ya gaza biyawa kudin makaranta a Cyprus – Gwamna Abba
A makonnin da suka gabata kuwa an riƙa sayar da dalar kan abin da ya haura naira 1,700 a kasuwannin bayan fage.
To amma ya zuwa ƙarshen makon da ya gabata farashin dala ya kama daga N1,535 a farashin gwamnati zuwa N1,555 a farashin ƴan kasuwa.
To sai dai yayin da hukumomi a Najeriyar, musamman babban bankin ƙasar CBN ke cewa matakan su ne suka kawo wannan sauyi da aka samu, masana na bayyana nasu ra’ayoyi da suka ci karo da wannan.
Masana irin su Shuaibu Idris na ganin cewa naira ta samu daraja ne kwanan nan saboda ”Najeriya ta karɓo wani bashin dala biliyan 2.2b daga kasuwar hada-hadar hannayen jari ta duniya kuma wannan ne ya sa dalar ta wadata a Najeriya ya kuma karya darajar ta a kan naira”.
Ya ce ”aiwatar da tsarin Electronic Foreign Exchange Matching System (EFEMS) ɗin abu ne da bai wuce mako ɗaya ba kuma bai kai lokacin da za a fara ganin alfanun sa ba kawo yanzu” domin shi harkar tattalin arziki ”tamkar shuka ƙwallon mangwaro ne wanda ke buƙatar lokaci mai tsawo kafin a amfana da shi.”
Mikati na ganin cewa wani abin da ya ƙara sanyawa aka samu ƙaruwar dala a kasuwa shi ne ƙaratowar ƙarshen shekara inda ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje ke komawa ƙasar ɗauke da dala.
Za a fuskanci hazo tsawon kwana uku a sassan Najeriya – NiMet
“Mazauna ƙasashen waje kan zo Najeriya ɗauke da daloli a irin wannan lokaci na ƙarshen shekara domin raba wa ƴan’uwa da abokan arziƙi.
Ɗorewar rashin tabbas
Shu’aibu Idris Mikati ya ce babu tabbas ko darajar naira za ta ci gaba da ɗagawa ko kuma a’a a wannan yanayi “kasancewar babu wani ƙwaƙƙwaran mataki ɗaya da aka ɗauka wanda zai tabbatar da ɗorewar haka.”
“Lamari na kasuwa abu ne da komai zai iya faruwa a kowane lokaci, kuma komai zai iya sauya, saboda haka babu wanda ya san abin da zai faru,” in ji masanin tattalin arziƙin.
Ba dai wannan ne karon farko da ake samun banbancin ra’ayi ba tsakanin gwamnatin Najeriya da masana tattalin arziki ba a game da alƙalumman tashi da saukar darajar naira, inda kowanne ɓangare ke bayar da ƙididdiga mai karo da juna a kai, kuma kowannensu na jajircewa a kan nasa bayanin.
Wannan na zuwa ne kuma a lokacin da jama’ar ƙasar ke ci gaba da kokawa a kan tsadar rayuwa da matsin tattalin arziki.