A yau safiyar Juma’a an tashi da ganin jami’an ƴansanda ɗauke da makamai tare da na DSS sun yi ƙawanya a Masarautar Kano, inda Sarki Muhammadu Sanusi ll ke zaune.
Rahotanni da jaridar kadaura24 ta samu sun nuna cewa jami’an tsaron sun hana shige da fice a gidan Sarkin.

Rahotanni sun baiyana cewa a yau din ake sa ran Sarki Sanusi zai raka sabon Wamban Kano, Munir Sanusi zuwa Bichi, inda zai yi hamkimci.
Haka a binciken da Jaridar Kadaura24 ta gudanar ta gano can ma fadar Bichi dake garin Bichi an zuba jami’an tsaro, mai yiwuwa da nufin hana zuwan sabon Wamban Kano da Sarki Sanusi II na nada .
Gwamnatin Kano ta Haɗa Kai da Ofishin Jakadancin Nijeriya a Indiya Don Inganta Walwalar Daliban Kano
An dai zara a yau sarki Sanusi II zai kai wanban na Kano a marsayin hakimin Bichi, ya kuma gudanar da zaman fadanci daga bisani ya jagoranci sallar juma’a a Babban masallacin masarautar ta Bichi.
Ga hotunan yadda gidan Sarki na Kofar kudu yake a wannan safiyar.
Ga kuma hotunan yadda gidan Sarkin Bichi yake a wannan safiyar