Duk da jami’an tsaro Sarki Sanusi II ya jagoranci zaman fada

Date:

Bayan da jami’an tsaro suka mamaye gidan Sarkin Rumfa, yanzu haka dai Sarkin Kano na 16 Malam Muhammad Sanusi II ya fito domin fara jagorantar zaman fada na Yau Juma’a a fadar Sarki da ke Kofar Kudu.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito da sanyin safiyar Juma’ar nan ne jami’an tsaro suka mamaye gidan Sarkin Kano, tare da hana Sarki Muhammadu Sunusi fita don tafiya masarautar Bichi.

Da fari Sarki Sanusi ya shirya jagorantar tawaga zuwa raka sabon hakimin Bichi zuwa masarautar Bichi, tare da gudanar da wasu aika-aikace da chan masarautar ta Bichi.

Talla

To amma tuni dubban jami’an tsaro suka mamaye fadar Sarki ta Kofar Kudu don hana Sarkin Fita zuwa ziyarar da ya shirya gudanarwa, Sannan chan Bichin ma an saka jami’an tsaro domin hana kowa shiga cikin gidan Sarkin na Bichi.

Masarautar Bichi dai na daga cikin masarautun da gwamantin jihar Kano ta ce ta soke , sai dai hakan yasa wadanda ba su yarda da matakin ba, suka garzaya kotu domin kalubalantar matakin.

Da dumi-dumi: Jami’an tsaro sun kewaye gidan Sarkin Kano Sanusi tare da hana shige da fice

Sai dai Rahotanni da Jaridar Kadaura24 ta samu sun nuna cewa yanzu haka Sarki Sanusi II ya zauna domin fara jagorantar zaman fada na Yau Juma’a kamar yadda ya saba gudanarwa.

Kawo yanzu dai babu wani jawabi a hukumance daga jami’an tsaro ta ruwaito cewa babu tabbacin suwa ne suka bayar da umarnin girke jamian tsaro a fadar Sarki da ke Kofar Kudu, amma zargi na alamta bangaren masu hamayya da gwamnatin Kano ne ke da hannu kan batun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...