Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba da kwazon daliban da gwamnatinsa ta dauki nauyin karatunsu domin karo ilimi a kasar Indiya.
A ziyarar da gwamna Yusuf ya kai wa daliban a jami’ar Sharjah da ke kasar Indiya, ya nuna matukar jin dadin sa da jajircewarsu da nasarorin da suka samu, inda ya bayyana nasarar da suka samu a matsayin hujjar dake bayyana fa’idar saka hannun jari a fannin ilimi.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa KADAURA24, gwamnan ya tabbatar da cewa an kashe kudaden da aka ware wa shirin bayar da tallafin karatu cikin hikima, saboda daliban ba su ba da kunya ba suna abun da aka tura su kuma sun ma zarce abin da ake tsammani saboda kwazon da suke.

Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da bunkasa ilimi, inda ya bayyana cewa, bunkasa rayuwar matasa shi ne babban jigon manufofin gwamnatinsa na ganin jihar Kano ta samu ci gaba.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa ziyarar tasa ta ba shi damar tattaunawa da daliban, tare da magance kalubalen da suke fuskanta da kuma tattara bayanai daga rukunin farko na dalibai sama da 400 da ya dauki nauyin karantunsu a jami’o’i daban-daban na Uganda da Indiya a wani bangare na shirin bayar da tallafin karatu na digiri ga matasa 1001.
A cewar sanarwar, ziyarar ta baiwa gwamnan damar auna nasarorin da aka samu wanda hakan ke nuna cewa za a cigaba da shirye-shirye domin tura rukunin na biyu har zuwa na ƙarshen don tabbatar da kammala shirin kai dalibai 1001 kasashen waje kafin ƙarshen zangon mulkinsa na farko.