Majalisar Dattawa ta dakatar da batu kan kudirin dokar Harajin Tinubu

Date:

Daga Sani Idris maiwaya

 

Majalisar Dattawan Nigeria ta ce ta dakatar da yin wani aiki akan dokar Harajin da shugaban Ζ™asa Bola Tinubu ya aike mata da shi.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito batun dokar harajin ya jawo ce-ce ku-ce akan kudirin dokar, wanda yan Arewacin Nigeria suke ganin idan aka tabbatar da dokar zata cutar da yankin sosai.

 

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Barau Jibrin ne ya sanar da hakan lokacin zaman majalisar na ranar Laraba.

Sanata Barau ya ce an umarci kwamitin kuΙ—i na majalisar ya dakatar da aikin da yake yi har sai wani kwamiti na musamman ya zauna da babban lauyan Ζ™asa kan kudirin dokar.

A makon da ya gabata ma majalisar wakilai ta Nigeriya ta dakatar da magana a akan batun dokar har illa-masha-Allah, sakamakon dambarwar da ta faru akan batun dokar harajin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related