Dalilai uku da suka sa aka dauke daurin auren yar Sarkin Bichi da dan Sanata Barau zuwa Abuja – Iyalan Sarkin Kano Ado Bayero

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Iyalan Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero sun bayyana cewa dauke daurin auren ‘yar Sarkin Bichi Alhaji Nasiru ado Bayero Wato Maryam wacce zata auri dan mataimakin shugaban majalisar Dattawan Nigeria Jibrin (Abba) Barau Jibrin daga Kano zuwa Abuja ba shi da wata alaka da batun Dokar Harajin da ake dambarwa akanta.

” An jawo hankalin mu cewa wasu a shafukan sada zumunta na zamani suna ta yadawa cewa an dauke daurin auren Maryam Nasiru Ado Bayero da Jibrin Barau Jibrin daga Kano zuwa Abuja ne saboda dambarwar da take faruwa kan dokar Harajin Tinubu, to muna sanar da duniya cewa wancan labarin ba gaskiya ba ne don haka jama’a su yi watsi da shi”.

Shugaban kwamitin tsare-tsaren yadda za a gudanar da bikin Alhaji Aminu Babba Danagundi Sarkin Dawaki Babba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sawa hannu kuma aka aikowa kadaura24 ranar litinin.

Talla

Ya ce an mayar da daurin auren zuwa Abuja ne kawai don manyan bakin da zasu halarci daurin auren daga ciki da wajen ƙasar nan su sami damar halartar taron ba tare da wani cikas ba.

” Dama bisa al’ada iyayen amarya su ne suke da ikon sanya inda za a daura auren yarsu, don haka Mun mayar da daurin auren ne don radin Kanmu ba don yar mu zata auri dan mataimakin shugaban majalisar Dattawan Nigeria ba”. Inji Amina Babba

Gidauniyar Awareness for human right and charity foundation ta bayar da kyautar jini leda 150 ga asibitin Murtala na Kano

Ya kara da cewa sauyawa wurin daurin auren ba shi da wata alaka ta kusa ko ta nesa da batun Dokar Haraji da take cigaba da yamutsa hazo a Nigeriya.

Aure Babban al’amari ne a addinin Musulunci Saboda sunna ce ta Annabi Muhammad Sallahu alaihi wasallam, don haka bai kamata a rika siyasantar da shi ba, a saboda muna kira ga al’umma da su yi watsi da wancan labarin ba shi da tushe ballantana makama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...